Ana ci-gaba da tashe tashen hankula tsakanin Hamas da Fatah a Gaza | Labarai | DW | 12.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da tashe tashen hankula tsakanin Hamas da Fatah a Gaza

´Yan bindiga na kungiyar Hamas sun kai hari kan hedkwatar abokiyar gabar kungiyar wato Fatah dake Gaza. Da farko jami´an Hamas sun bawa mayakan Fatah wa´adin sa´o´i biyu da su fice daga wuraren tsaro masu muhimmanci. Kamfanonin dillancin labaru sun ce Hamas ta fara mamaye wasu sansanoni na Fatah dake arewaci da tsakiyar Gaza. A ci-gaba da kaiwa juna hare haren ramuwar gayya, mayakan Fatah sun kai hari kanw ata tashar telebijin ta Hamas. A wani lokaci nan gaba kungiyar Fatah ta shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas zata yanke shawara ko ta fice daga cikin gwamnatin hadin guiwa da ta kafa da Hamas kimanin watanni 3 da suka wuce. Wannan matakin ya biyo bayan mutuwar mutane 18 sakamakon tashe tashen hankula a Gaza a cikin sa´o´i 24. Hakan kuwa na faruwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma jiya daddare.