Ana ci gaba da shari’ar Saddam Hussein a birnin Bagadaza. | Labarai | DW | 15.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da shari’ar Saddam Hussein a birnin Bagadaza.

Yau ne ake ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussein, a birnin Bagadaza tare da wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa guda 7, waɗanda gaba ɗaya ake tuhumarsu da aikata miyagun laifuffuka kan bil’Adama. Rahotannin da ke iso mana daga birnin sun ce Saddam Hussein ya ƙi amsa laifin da ake zarginsa da shi. Ƙararrakin da aka ɗauka gaban kotun game da Saddam Hussein sun haɗa ne da yi wa wasu ’yan ƙauyen Dujail, su 148, mabiya ɗariƙar shi’iti kisan gilla a tsakiyar shekarun 1980. Kazalika kuma ana zarginsa da azabtad da mata da yara da yawa daga wannan yankin. Shi dai Saddam ya faɗa wa kotun cewa, ba zai amsa ƙararrakin ba, saboda a wannan lokacin, shi ne shugaban Iraqi. Ana dai sa ran a yau ɗin ne za a kira shaidu don yi wa kotun nasu bayanan.