Ana ci-gaba da samun tangarɗa a zurga-zurgar jiragen sama a Turai | Labarai | DW | 17.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da samun tangarɗa a zurga-zurgar jiragen sama a Turai

Har yanzu gajimaren toka na ci-gaba da kawo cikas a zurga-zurgar jiragen sama

default

Fasinjoji za su ci gaba da jiran tsammani warabbuka a filayen jiragen sama

Ɗaukacin nahiyar Turai na ci-gaba da zama wani wurin da aka hana zurga-zurgar jiragen sama yayin da gajimaren toka daga wani dutse dake amar wuta a ƙasar Iceland ke ci-gaba da tirniƙe sararin samaniyar Turai. Hukumomin kula sufurin jiragen sama a ƙasashen Turai da dama na tsammanin za a ci-gaba da soke tashi da saukan jiragen sama a yau Asabar. Yanzu haka dai an rufe dukkan filayen jiragen sama 16 a Jamus, sannan filayen jiragen sama a ƙasashen Faransa, Birtaniya da kuma Netherlands za su kasance a rufe a yau. An kiyasce cewa wannan matsalar na jawowa kamfanonin zurga-zurgar jiragen saman da abin ya shafa, asara dala miliyan 200 a kowace rana. A kuma halin da ake ciki Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya soke wata tafiya da ya shirya zuwa Janhuriyar Demokuraɗiyyar Kongo yana mai nuni da taɓarɓarewar zurga-zurgar jiragen saman a ƙasashen Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala