1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da raya ranar mata ta duniya

A ci gaba da raya ranar mata ta Mdd, dubbannin mata ne suka gudanar da wani gagarumin taro a Pakistan don raya wannan rana.

Taron wanda ya gudana a karkashin jagorancin yar gwagarmayar neman yancin matan nan wato Mukhtaran Mai, an kiyasta cewa ya samu halartar mata a kalla dubu uku.

Lokacin da take jawabi ga matan , Mai yar shekaru 33, tayi alkawarin ci gaba da gwagwarmaya na nemowa mata yancin su matukar tana raye.

Duk da cewa an hana matan gudanar da maci a akan tituna, da yawa daga cikin matan sun bukaci gwamnatoci su tabbatar musu da yancin su a hannu daya kuma da girmama su.

Rahotanni daga kasar ta Pakistan sun nunar da cewa an gudanar da tarurruka da kuma gabatar da kasidu a garuruwa daban daban na kasar don raya wannan rana.