1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da musayar wuta tsakani Isra´ila da dakarun Hisbollah

July 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buq6

Duk da kokarin da ake yi don warware wannan rikici ta hanyoyin diplomasiya, jiragen saman yakin Isra´ila da ´yan Hisbollah a Libanon na ci-gaba da kaiwa juna hare hare. A yau talata an harba rokoki akan wurare da dama dake arewacin Isra´ila, musamman a biranen Safed da Haifa da Nahariya da Schlomi da kuma Tiberia. To sai dai babu labarin wadanda suka jikata. Amma a bangaren Libanon akalla mutane 19 sun rasu sakamakon hare-haren da jiragen saman Isra´ila suka kai kan sansanonin soji da unguwannin fararen hula a cikin Libanon. A kuma halin da ake ciki ana ci-gaba da kwashe baki ´yan kasashen waje daga Libanon. Wani jirgin ruwa da Faransa ta yi catarsa ya tashi daga Libanon dauke da mutane 950 zuwa Cyprus. Sannan dazu dazun nan kuma wani jirgin sama dauke da Jamusawa kimanin 300 da suka tsere daga rikicin na Libanon, ya sauka a filin jirgin sama na birnin Dusseldorf.