1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da musayar wuta tsakani Isra´ila da dakarun Hisbollah

July 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bupf
A ci-gaba da hare haren da ta ke kaiwa Libanon, a karon farko a yau jiragen saman yakin isra´ila sun kai farmaki a yankunan mabiya addinin Kirista dake tsakiya da kuma arewacin Libanon. Jiragen saman yakin Yahudun Isra´ila sun lalata nau´rori da hasumiyar kafofin yada labaru da na wayoyin salula a garin Adma dake arewa da birnin Beirut. ´Yan sanda sun nunar da cewa tashar telebijin ta LBC mai zaman kanta ta katse shirye shiryenta na wasu dakiko. Harin ya kuma shafi tashar telebijin Al-Manar ta ´yan Hisbollah. A halin da ake ciki rundunar sojin Isra´ila ta ce a yakin da take yi da ´yan Hisbollah yanzu zata kayyade wuraren da take kutsawa ciki a Libanon kuma ba ta shirin yin wani kutse mai girma daga dakarunta na kasa. Tuni dai sakatare janar na MDD Kofi Annan yayi gargadi game da wani mamaye, wanda ya ce zai kara tsananta mummunan halin da ake ciki. A cikin sa´o´io 24 da suka wuce dai jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hare hare har 150 a cikin Libanon. Yayin da ´yan Hisbollah kuma suka harba rokoki akalla 35 cikin arewacin Isra´ila a yau asabar.