1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da musayar wuta a sansanin ´yan gudun hijirar Falasdinawa a Libanon

Tankokin yakin Libanon na ci-gaba da yin lugudan wuta akan wani sansanin ´yan gudun hijirar Falasdinawa dake arewacin wannan kasa kwana na biyu a jere. Sojojin kasar na fafatawa da ´yan takifen kungiyar fatah al-Islam wadda ake zargin ta da alaka da kungiyar al-Qaida da kuma masu matsanancin ra´ayi na Syria. A yau litinin Syria ta yi watsi da zargin da jami´an Libanon ke yi cewa ta na da alaka da kungiyar ta Fatah al-Islam. Majiyoyi a cikin sansanin sun ce an halaka fararen hula 9 a lugudan wutar ta yau litinin. A jimilce dai an halaka mutane akalla 55 a gumurzun baki daya.