1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da macin nuna adawa da gwamnati sojin Myanmar

September 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuAW
Kimanin mutane 10 dubu karkashin jagorancin dubban ´yan addinin Bhudda sun yi wani maci a babban birnin kasar Myanmar, Yangon don nuna bijirewar su ga gwamnatin mulkin sojin kasar. Wannan macin ya zo ne kwana guda bayan da shugabar ´yan adawar Myanmar Aung San Suu Shi ta jinjinawa ´yan addinin na Bhudda lokacin da suka wucewa ta kofar gidan da ake yi mata daurin talala tuna shekara ta 2003. Shugabannin masu zanga zangar sun lashi takobin ci-gaba da maci har sai gwamnatin mulkin sojin ta ruguje. A cikin watan jiya aka fara zanga-zangar bayan da gwamnati ta ninka farashin man fetir har sau biyu.