1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ana ci gaba da kokarin kwato jamiin jamus da aka sace a Yemen

Jamian kasar Yemen sun sake jaddada tabbacinsu cewa nan bada jimawa ba zasu samu nasasar sako tsohon jamiin diplomasiya na Jamus da iyalinsa da aka sace a kasar.

Jürgen Chrobog da mai dakinsa tare da yaransu boyu an sace su ne a farkon wannan mako a kasar ta Yemen bayan wata gaiyata da tsohon jakadan Yemen a Jamus yayi masu.

Rahotanni sunce wasu yan bindiga ne na kabilar al_Abdulla suka sace su,suna masu neman a sako wasu yan uwansu 5 dake dauru a gidan yari.

Jamian ofishin jakadancin Jamus a Yemen sunce sunyi magana da Chrobog ta wayar tarho,kuma ya basu tabbacin cewa shi da iyalin nasa suna cikin koshin lafiya.

Jamian na Yemen sunce zasu bi bi hanyar lumana da diplomasiya wajen kwato su.