Ana ci gaba da kirga kuriu a Iraqi | Labarai | DW | 16.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kirga kuriu a Iraqi

Ana nan ana ci gaba da kirga kuriu kusan miliyan 11 a zaben kasar iraqi da aka gudanar jiya alhamis,zabe na farko tun hambarar da gwamnatin Saddam Hussein a 2003.

Jamian zaben sunce ya zuwa yanzu dai sun samu koke koke a game da yan sanda da jamian tsaro,amma babu wani koke akan magudi ko laifukan zabe.

Shugaba Bush na Amurka yace wannan zabe wani babban mataki ne na komawa kan tafarkin demokradiya.

Kasashen Australia da Japan kuma cewa sukayi fitowar jamaa da dama su kada kuriar, ya kawadda laifin kaiwa kasar yaki.

Yan sunni wadanda yawancinsu suka kauracewa zaben watan janairu,sun fito da dama a wanan karo sun jefa kuriarsu.

Nan gaba cikin wannan wata ne ake sa ran samun sakamakon zaben.