Ana ci gaba da kashe kashe a Iraqi | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kashe kashe a Iraqi

Yan bindiga a Iraqi sun kashe wasu yan shia 22 a garin Diyala yayinda tashe tashen hankula ke ci gaba a kasar ta Iraqi.

Rahotanni sunce yan bindigar sun kai farmaki ne cikin wasu gidaje biyu a garin na Diyala inda suka fito da maza 21 daga wadannan gidaje suka harbe su.

Wannan hari yazo ne bayan kashe wasu mutane fiye da 200 da akayi cikin wani harin bam a birnin Bagadaza da kuma fada a birnin Sadr.

Yanzu haka an shiga kwana na biyu na hana fita a birnin na Bagdaza.

Dole kuma shugaba Jalal Talbani ya dakatar da ziyararsa zuwa Tehran saboda birnin Bagdaza yana rufe.

Yace zai kai wannan ziyara ce zuwa Iran don tattauna kann irin rawar da Iran zata taka wajen magance tashe tashen hankula a Iraq da zarar an bude filin jirgin saman Bagadaza.