Ana ci-gaba da kai hare haren ta´addanci a Iraki | Labarai | DW | 24.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da kai hare haren ta´addanci a Iraki

Kwana daya bayan jerin munanan hare haren da aka kai a birnin Bagadaza, a yau wasu maharan kunar bakin su biyu sun kashe mutane 22 a arewacin Iraqi. An kai sabbin hae haren ne kuwa a garin Tal Afar. Yanzu haka dai yawan wadanda suka rasu harin bama-baman da aka kai jiya a unguwar Sadr City dake birnin na Bagadaza ya kai mutum 202. Likitoci sun ce yawan wadanda suka mutu zai karu saboda da ganin cewa da yawa daga cikin mutum 260 suka samu raunuka ba zasu yi rai ba. duk da dokar hana fita da aka kafa a birnin na Bagadaza, an yi jana´izar mutanen a unguwar ta Sadr City.