1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da kai hare haren bama-bamai a Bagadaza

Wasu jerin hare haren makamai masu linzami da aka kai kan unguwar Adhamiyah ta ´yan Sunni dake birnin Bagadaza sun halaka mutane 15 sannan wasu 56 sun samu raunuka. Wani likita ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarun AFP da haka, to amma jami´an tsaron Iraqi duk da cewa sun tabbatar da kai hare haren amma sun ki su ce uffan game da wadanda abin ya rutsa da su. Hare haren sun zo ne kwana guda bayan wani mummunan harin bam da aka kai da wata babbar mota a unguwar Al-Sadiriya dake tsakiyar Bagadaza ya halaka mutane 130 yayin da wasu daruruwa suka jikata. A yau lahadi akalla mutane 20 aka kashe a wasu hare haren bama-bamai a ciki da wajen Bagadaza.