Ana ci gaba da kai hare-hare a Iraqi. | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kai hare-hare a Iraqi.

A wata sabuwa kuma, hukumar ’yan sandan Iraqi ta ba da sanarwar cewa wani bam da aka ta da cikin mota, ya janyo asarar rayukan mutane 10, dukkansu fararen hula. An ta da bam ɗin ne gaban wani banki a garin Suweira da ke kudu maso gabashin birnin Bagadaza mai rinjayin mabiya ɗariƙar shi’iti, inji sanarwar. Mutane 15 ne kuma suka ji rauni. A birnin Bagadazan da kansa ma, rahotanni sun ce an ta da bamabamai biyu a gefen titi, waɗanda suka halakad da ɗan sanda ɗaya, sa’annan kuma suka ji wa wasu 7 rauni. Har ila yau dai jami’an tsaro sun ce sun gano gawawwakin a ƙalla mutane 8 a kewayen birnin Bagadazan, waɗanda aka bindige. Hukumar rundunar sojin Amirkan kuma ta tabbatar cewa, an sake kashe wasu sojojinta guda 3, a ɗaukin da suke yi da ’yan yaƙin gwagwarmaya a Iraqin, abin da ya kawo yawan sojojin Amirkan da aka kashe a Iraqin a cikin wannan watan zuwa 53.