Ana ci gaba da haɓakar tashe-tashen hankulla a Iraqi. | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da haɓakar tashe-tashen hankulla a Iraqi.

A Iraqi, har ila yau dai ƙurar rikicin da ke barazanar sanya ƙasar cikin yakin basasa ta ƙi lafawa. Rahotannin baya bayan nan da muka samu daga birnin Bagadaza sun ce a jerin hare-haren bindiga da bamabamai da rokoki da ’yan yaƙin gwagwarmayar ƙasar suka kai a yankuna daban-daban na birnin, mutane 13 ne suka rasa rayukansu. Jami’an gwamnatin ƙasar sun ce da sanyin safiyar yau, wasu ’yan bindiga sun afka wa wani gidan gasa burodi na mabiya ɗariƙar shi’iti, inda suka kashe mutane 8 kai tsaye, sa’annan suka ji wa mutum ɗaya kuma rauni. A yau ɗin ne kuma dai wasu bamabaman da aka dasa a gefen titi a birnin na Bagadaza, suka tashi, inda suka halakad da wani ɗan sandan Iraqin da wani farar hula, sa’annan wasu mutane 3 kuma suka ji rauni. A gabashin birnin kuma, rahotanni sun ce wasu rokoki biyu da aka harba sun, daki gun da ’yan sanda suka tare suna binciken motoci, a kusa da ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar. A nan ma, mutum ɗaya ne ya rasa ransa, sa’annan wani mutum ɗaya kuma ya ji rauni. Har ila yau dai, rahotannin sun ce wasu sojojin Amirka biyu sun sheƙa lahira, a wata fafatawar da rukuninsu ya yi da ’yan bindiga yau a birnin na Bagadaza.