Ana ci-gaba da gwabza fada a birnin Mogadishu | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da gwabza fada a birnin Mogadishu

Wani kazamin fada da manyan bindigo ya sake barkewa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia tsakanin dakarun ´yan ra´ayin Islama da madugan yaki wadanda Amirka ke goyawa baya. Rahotanni sun nunar da cewa akalla mutane 20 sun rasu a wannan kazamin fada da aka gwabza yau. Hakan dai ya kawo yawan wadanda aka kashe tun bayan barkewar sabon fadan a ranar laraba ya zuwa akalla mutum 70. A jiya da daddare an samu lafawar wannan fada, to amma da sanyin safiyar yau an wayi gari da jin karar aman bindigogin atileri da harba makamai masu linzami a unguwannin Daynile da kuma Keysaney dukkan su a birnin Mogadishu.