1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da gumurzu a garin Biltine dake gabashin Chadi

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYd
Sojojin Chadi sun gwabza kazamin fada na tsawon sa´o´i da dama da ´yan tawaye a gabashin kasar. An yi gumurzun ne a wani wuri mai nisan kilomita 50 dake wajen garin Biltine, wanda ´yan tawayen kungiyar UFDD suka kwace kwace a ranar alhamis, gabanin su janye kwana guda baya, saboda dannawar da sojojin gwamnati ke yi. Madugun ´yan tawaye Mahamat Nouri ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa wasu ayarin motocin sojin gwamnati sun yiwa mayakansa kawanya kafin su kai musu hari. Ya ce bayan an gwabaza kazamin fada dakarunsa sun fatattaki na gwamnati inda suka kashe sojoji 200 sannan su kuma suka yi asarar mutum 50. Wata majiyar sojin Chadi ta tabbatar da gwabza fadan a wajen garin na Biltine amma ta ki ba da yawan mutanen da aka kashe.