Ana ci gaba da fama da matsalar yunwa a sassa daban-daban na duniya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.10.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ana ci gaba da fama da matsalar yunwa a sassa daban-daban na duniya

Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya akan matsalar yunwa a duniya shi ne ya shiga kannun rahotannin jaridun Jamus a wannan makon

default

Mata sun yi cincirindo gaban ofishin taimakon agaji ta Welthungerhilfe a Mafagaskar

A wannan makon rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya akan matsalar yunwa a duniya shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus. A cikin nata rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung ta fi mayar da hankali ne akan kiran da aka yi na ƙarfafa matsayin mata a fafutukar yaƙar matsaloli na talauci da yunwa a ƙasashe matasa. Jaridar ta ce:

"Ɗaya daga cikin muhimman matakan yaƙi da matsalar ƙarancin abincin dake addabar mutane kimanin miliyan dubu ɗaya a sassa daban-daban na duniya shi ne ƙarfafa matsayin mata, musamman a ƙasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Akwai barazanar fuskantar matsalar yunwa mafi muni irinta a cikin wannan ƙarni muddin ba a ɗauki matakan kadagarkinta ba. Ƙasashen Afirka da matsalar ta fi shafa yanzu haka sun haɗa da Burundi da Janhuriyar Demoƙraɗiyar kongo da Eritrea da Saliyo da Chadi da kuma Habasha, waɗanda ƙasashe ne da suka sha fama da yaƙi. To sai dai kuma rashin shugabanci na gari da kuma cutar nan ta Aids mai karya garkuwar jiki na daga cikin ummalaba'isin matsalar ta yunwa."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta ba da la'akari ne da halin da ake ciki a Somaliya, wadda rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya bai ma taɓo ta ba. Jaridar ta ce:

Selbstmordanschlag in Magadischu Somalia

Rikici a Somaliya na daga cikin dalilin matsalar yunwa a ƙasar

"Somaliya ce ta fi fama da raɗaɗin yunwa tsakanin ƙasashen Afirka, inda kimanin kashi ɗaya bisa uku na al'umarta ke cikin mawuyacin hali na rayuwa. Tun bayan tumɓuke gwamnatin Somaliyar shekaru goma sha takwas da suka wuce ba a taɓa fuskantar mawuyacin hali irin shigen wanda ake ciki yanzu ba. Amma kuma ba yaƙin basasar ƙasar ne kaɗai musabbabin haka ba, kazalika ana fama da ƙarancin ruwan sama a yankuna masu danshi na ƙasar, inda ƙurar yaƙin ba ta yaɗu cikinsu ba."

A Afirka ta Kudu, a daidai lokacin da ƙasar ke shirye-shiryen karɓar baƙoncin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya gwamnati ta ba da sanarwar niyyarta ta ƙara farashin wutar lantarki. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi bayani akan haka tana mai cewar:

"Ƙasar Afirka ta Kudu, wadda ta fi kowace ƙasa a nahiyar Afirka ƙarfin tattalin arziƙi tayi shekara da shekaru tana fama da matsalar wutar lantarki. Gwamnati ta yi sako-sako da manufofin inganta hanyoyin sadarwa a cikin shekarun 1990 duk da ƙaruwar yawan jama'a da kuma bunƙasar tattalin arziƙin da ta samu, wadda bata taɓa ganin shigenta ba a cikin tarihinta. Kazalika an yi watsi da matakan gyare-gyare ga tashoshin lantarki na ƙasar, wanda a sakamakon haka aka sha fama da matsalar wuta, lamarin da a ɗaya ɓangaren ya haifar da asarar dubban miliyoyi na dalar Amurka ga tattalin arziƙin wannan ƙasa."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal