Ana ci gaba da fafatawa tsakanin Hamas da Fatah a Gaza | Labarai | DW | 13.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin Hamas da Fatah a Gaza

Fada na ci gaba da yin muni tsakanin bangarorin adawa na Hamas da Fatah a yankin Palasdinawa inda ya zuwa yanzu mutane akalla 53 suka rasa rayukansu tun ranar asabar.

A jiya talata yan bindiga na Hamas sun farma yankunan yan kungiyar Fatah a zirin Gaza inda suka kamme manyan sansanonin yankin.

Yanzu haka dai ministocin gwamnatin hadaka yan kungiyar Fatah sunyi barazanar jingine hulda da Hamas har sai an kawo karshen tashe tashen hankula tukuna.

Shugaba Mahmud Abbas wanda kuma shine shugaban kungiyar Fatah ya zargi shugabanin Hamas da shirya juyin mulki na soja.

KTT dai tayi gargadi game da yiwuwar barkewar yakin basasa a yankin na Palasdinawa.