Ana ci gaba da fada a Mogadishu | Labarai | DW | 30.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da fada a Mogadishu

Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu cikin wani faɗa tsakanin dakarun dake goyon bayan gwamnati da `yan tawaye a arewacin Mogadishu.Wadanda suka ganewa idanunsu sunce a cikin faɗan wanda shine mafi muni cikin fiye da mako guda dakarun Habasha da suke marawa gwamnatin wucin gadin Somalia baya sun kara da sojojin sa kai a unguwar Suqa Holaha,kuma fararen hula ne duka suka rasa rayukan nasu.Sai dai kuma rundunar sojin Somalia tace dukkaninsu sojojin sa kai ne.Rundunar sojin ta Somalia ta ce har yanzu sojojinta suna ci gaba da ɗauki a arewacin birnin na Mogadishu.