Ana ci-gaba da dauki ba dadi tsakanin matasa da ´yan sanda a Paris | Labarai | DW | 04.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da dauki ba dadi tsakanin matasa da ´yan sanda a Paris

Har yanzu ana fama da dauki ba dadi tsakanin matasa da jami´an tsaro a unguwannin dake wajen Paris babban birnin Faransa. Rahotanni daga unguwar Seine-Saint-Denis matasa masu ta da kayar baya sun cunnawa motoci da dama wuta tare da harbi akan motoci ´yan sanda. Yanzu haka dai an girke jami´an tsaro kimanin dubu 1 da 300 don kawo karshen wannan arangama da aka shafe kwanaki 7 a jere ana yi. FM Faransa Dominique De Villepin ya ce ba zai mika wuya ba kana kuma gwamnati ba zata yi sako sako wajen daukar matakan da suka dace kan masu ta da zaune tsayen ba. Da farko shugaban kasa Jacques Chirac ya yi kira ga jama´a dake zaune a wadannan unguwanni na talakawa da su kwantar da hankalinsu, to amma ba´a ji wannan kira ba. Rikicin dai ya barke ne bayan mutuwar wasu matasa biyu wadanda ke tserewa binciken ´yan sanda.