Ana ci-gaba da daukar matakan tsaro a Birtaniya | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da daukar matakan tsaro a Birtaniya

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad

Pakistan ta ba da sunan wani dan Birtaniya wanda ake zargi da alaka da kungiyar al-Qaida, wanda ake gani ya na da hannu a wani shiri da aka yi na dana bama-bamai cikin wasu jiragen sama a Birtaniya. Ma´aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce Rashid Rauf wanda ke cikin mutanen da aka kama baya bayan nan a kasar, ya na da alaka da wadanda suka yi shirin kulla wannan makarkashiya. A lokacin da yake magana kwana guda bayan da hukumomin Birtaniya suka bankado wannan makarkashiya ta tarwatsa jiragen sama da suka kai 10 akan hanya daga Birtaniya zuwa Amirka, sakataren cikin gida John Reid ya ce za´a ci-gaba da tsaurara matakan tsaro. Kawo yanzu ´yan sandan Birtaniya sun kama mutane 24 daukacin su musulmi ´yan Birtaniya.