1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da batakashi a Mogadishu babban birnin Somalia

Ana ci-gaba da gwabza mummunan fada a Mogadishu babban birnin Somalia tsakanin sojojin sa kan musulmi da wani kawance madugan yaki kwana shida a jere. An jiwa akalla karin mutane biyu rauni a bata-kashi da aka yi yau juma´a, abin da ya kawo yawan wadanda suka samu raunuka zuwa mutum 200 yayin da 80 suka wkanta dama. A halin da ake ciki dubban mutane sun tsere daga yankunan arewa da kuma tsakiyar babban birnin na Somalia. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun bayyana rikicin baya bayan nan da cewa shi ne mafi muni a tsawon shekaru sama da 10 da aka kwashe ana fama da rigingimu da rashin bin doka da oda a cikin kasar. MDD da kuma gwamnatin wucin gadin Somalia sun yi kira da masu bawa hamata iska da su kwantar da hankullansu.