1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da ba ta kashi tsakanin dakarun ƙetare da ’yan ƙungiyar Taliban a Afghanistan.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burl

Jiragen saman yaƙin dakarun ƙawance na ƙasashen ƙetare da ke girke a Afghanistan, sun kai hari kan guraban mayaƙan kungiyar Taliban, inda bisa cewar rundunar, suka kashe ’yan Taliban ɗin guda 8. Hakan dai ya biyo bayan kashe wasu sojojin Birtaniya guda biyu da tafintansu, dan ƙasar Afghanistan ɗin ne, jiya, da ’yan ƙungiyar Taliban suka yi, a wani harin da suka kai musu a jihar Helmand da ke kudancin ƙasar. Ana ta ƙara samun tashe-tashen hankulla a jihar ne, a daidai lokacin da ƙungiyar NATO ke shirin karɓar jagorancin dakarun ƙetare a Afghanistan daga hannun rundunar sojin Amirka.

Tun watan Janairun wannan shekarar dai, kusan mutane dubu ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulla a ƙasar. Alƙaluma na nuna cewa yawan dakarun ƙetare da aka kashe a cikin wannan lokacin, ya kai 50.