Ana ci-gaba da artabu tsakanin sojojin Libanon da ´ya´yan Fatah al-Islam | Labarai | DW | 02.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da artabu tsakanin sojojin Libanon da ´ya´yan Fatah al-Islam

Sojojin Libanon sun na ci-gaba da yin lugudan wuta akan masu tsauttsuran ra´ayin na Islama a wani sansanin ´yan gudun hijirar Falasdinawa dake kusa da birnin Tripoli. An yi ta karar manyan bindigogi da sanyin safiyar yau asabar, kwana guda bayan wani kazamin fada da yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 19 a sansanin na Nahr el-Bared. Ministan sadarwa na Libanon ya fadawa tasahr DW cewa sojojin na yaki ne da ´yan takifen kungiyar Fatah al-Islam, wadanda rahotanni suka ce suna da alaka da kungiyar Al-Qaida. A halin da ake ciki sojojin Libanon sun yi kira da ´ya´yan kungiyar da su yi saranda sannan ka da mazauna wannan sansani su ba su mafaka.