Ana ci-gaba da artabu tsakanin sojin gwamnati da ´yan tawayen Tamil | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da artabu tsakanin sojin gwamnati da ´yan tawayen Tamil

Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta ce ta sake gwabza sabon fada a cikin ruwa da ´yan tawayen Tamil Tigers, inda sojojinta suka lalata kwale-kwalen biyu sannan suka halaka ´yan tawaye akalla su 6. Rundunar ta ce ta katse hanzarin ´yan tawayen ne lokacin da suka kusanci sansanin sojin ruwan dake tsibirin Kyats na yankin Jaffna. A jiya juma´a ma rundunar ruwan ta lalata kwale-kwale 15 sannan ta halaka ´yan tawayen Tamil Tigers su 35. A halin da ake ciki ´yan tawayne sun tabbatar da cewa an gwabza fadan amma ba su ce uffan game da rashin sojojin su da suka yi ba. Duk da sabbin tashe tashen hankulan, dukkan sassan biyu sun nuna aniyarsu ta halartar shawarwarin samar da zaman lafiya da za´a yi a Geneva a ranakun 28 da 29 na wannan wata.