Ana ci-gaba da aikin ceto bayan hadarin jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da aikin ceto bayan hadarin jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya

Ana fargabar cewa sama da mutane dubu daya suka rasu sakamakon mummunan hadarin jirgin ruwa a tekun Bahar-Maliya. Kafin safiyar yau asabar jami´ai sun ce an ceto rayukan mutane 340 daga cikin fasinjoji kimanin dubu daya da 400 dake cikin jirgin ruwa lokacin da ya nitse a wani wuri mai tazara kilomita 70 da gabar tekun Masar. An kuma tono gawawwaki 200. A ranar alhamis da dare jirgin ruwan ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta Duba dake Saudiya zuwa tashar jirgin ruwa ta Safaga dake Masar, amma aka bar jin duriyarsa. Daukacin fasinjojin dake cikin jirgin dai mahajjata ne dake komawa gida bayan kammala aikin hajjin bana. Yayin sauran kuma suka kunshi ´yan ci-rani na Masar dake aiki a kasa mai tsarki. Wadanda suka tsira daga hadarin sun ce gobara ta tashi a cikin jirgin kafin ya nitse. Watakila kuma rashin kyawan yanayi na daga cikin dalilan da suka haddasa hadarin. Shugaban Jamus Horst Köhler da SG Angela Merkel sun aike da jajensu ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.