Ana ci-gaba da aikin ceto a hadarin jirgin ruwa a Masar | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da aikin ceto a hadarin jirgin ruwa a Masar

Har yanzu ma´aikatan ceto a Masar na ci-gaba da aikin ceto wadanda watakila ke da sauran numfashi a mummunan hadarin jirgin ruwan nan da ya auku a tekun Bahar Maliya a jiya juma´a. Yawan wadanda aka ceto yanzu yana tsakanin mutum 389 zuwa 435, sannan an tono gawawwaki kimanin 180 yayin da har yanzu ba´a ga mutane kimanin 900 ba. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce wata gobara ta tashi a cikin jirgin ruwan jim kadan bayan tashin sa daga tashar jirgin ruwa ta Duba dake Saudiya. Jirgin wanda ke kan hanya zuwa Safaga dake kasar Masar, ya nitse ne a wani wuri mai tazarar kilomita 100 kudu maso gabashin wurin shakatawa na bakin teku dake Hurghada. Mutane dake neman bayanai game da dangin su da hadarin ya rutsa da su sun rushe shingayen da ´yan sanda suka kakkafa don toshe hanyoyi.