1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana bukatar biliyoyin daloli don kare Afrika daga dumamar yanayi

Hauwa Abubakar AjejeNovember 7, 2006

Taron Majalisar dinkin duniya akan canjin yanayi da ake gudanarwa a Nairobin kasar Kenya,yace canjin yanayi zaiyi kaca kaca da nahiyar Afrika,idan sauran kasashen duniya basu taimaka mata bat a wannan fanni.

https://p.dw.com/p/BtxW
Hoto: picture-alliance/dpa

A cewar kakakin hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya,Nick Nuttall,nahiyar Afrika itace nahiya da take baya wajen gurbata yanayi,amma kuma canjin yanain ita zai fi shafa.

Ya fadawa manema labarai cewa,sabbin binciken kimiya da aka gudanar sun baiyana cewa,illar canjin yanayin zai shafi Afrika fiye da yadda tun farko ake zato.

Rahoton ya gano cewa mutane miliyan 70 da kuma kashi 30 cikin dari na albarkatun bakin ruwa a nahiyar Afrika suke fuskantar bala’in ambaliyar ruwa a 2080 sakamakon tumbatsar tekuna,fiye da kashi 1 bisa uku na namun daji zasu halaka yayinda albarkatun gona zasu ragu sakamakon dumamar yanayi da fari.

Zuwa 2025,mutane miliyan 480 ne a Afrika zasu kasance a yankunan da ake karancin ruwan sha.

Nuttal yace Afrika itace nahiya dake baya da bata shiryawa canjin yanayi ba,saboda haka tana bukatar taimako daga kasashen duniya.

Mataimakin shugaban kasar Kenya Moody Awori,yace dole ne kasashen Afrika su kudiri aniyar kare albarkatunsu,don kare fadawa cikin balai

Haka shima babban darektan hukumar kula da yanayin ta MDD Achim Steiner cewa yayi,dole ne manyan kasashen duniya su taimakawa kasashen da suka fi fuskantar wannan matsala a cikin nahiyar Afrika.

Yace Afrika tana ci gaba a fannonin tattalin arziki,tana gina hanyoyi,layin jiragen kasa da kuma tashoshin ruwa,amma ya kamata a gina su ta hanyar dab a zasu lalace cikin shekaru 30 zuwa 40 ba,saboda canjin yanayi.

Wadannan illoli a cewar rahoton da gwamnatin Burtaniya ta fitar a makon daya gabata,zasu shafi tattalin arzikin duniya,inda tace tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi 20 cikin dari,cikin hali mafi muni.

Masana kimiya sun kiyasta cewa,ana bukatar rage yawan hayakin masanaantu da kashi 80 cikin dari kafin 2050 don kare illoli dab a zaa iya magance sub a.

Karkashin yarjejeniyar Kyoto,kasashe 25 da suka ci gaba,banda Amurka da Australia,sunyi alkawarin rage hayakin masanaantunsu da kashi 5 zuwa 2012,amma a wasu kasashen na Kyoto kamar Spain da Canada sai karuwa abin yake yi maimakon raguwa,kasar Canada dai tuni ma tace ba zata iya cimma abinda tayi alkawarin ba.

Mahalarta taron na birnin Nairobi zasu kwashe makonni 2 suna tattaunawa akan yadda zaa kaddamar da yarjejeniyar ta Kyoto,musamman samarda kudaden da zaayi anfani da su.

Karkashin yarjejeniyar dai kasashe da suka ci gaba zasu rika sanya kudi a cikin asusun Kyoto,kimanin dala miliyan 30 zuwa 40 a kowace shekara fara daga 2008.

Sai dai masana kimiya sun baiyana cewa,ba tare da rage yawan hayakin masanaantun ba babu abinda wadannan kudade zasu anfanar.

Steve Sawyer na kungiyar Green peace yace abu mafi muhimmanci da ake bukata yanzu shine kasashe dake da arzikin masanaantu su rage hayakin masaantunsu tare da taimakawa kasashe matalauta.

Yace,kodayake babu wanda yake sa ran Amurka wadda tafi kowace kasa a duniya fitar da hayaki mai guba na masanaantu,zata yi wani abu akai,har sai an samu sabuwar gwamnati da zata maye fadar white house nan gaba.