Ana bincike game da kisan Kim Jong-Nam | Labarai | DW | 15.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana bincike game da kisan Kim Jong-Nam

An hallaka mutumin da aka yi imanin Kim Jong-Nam ne dan uwan shugaban Koriya ta Arewa sakamakon allurar mutuwa Malesiya.

Hukumomi a Malesiya sun kaddamar da binciken kisan da aka yi wa Kim Jong-Nam dan uwan shugaban Koriya ta Arewa da ake zargin wasu mata wakilan gwamnatin Koriya ta Arewa da aikatawa.

Hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu ta ce Marigayi Kim Jong-Nam da ke zama dan-uwan shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya dade ya na neman kariyar lafiya, tun bayan yunkurin hallaka shi a shekara ta 2012. Shugaban hukumar leken asiri ya sanar da haka ga majalisar dokoki. Koriya ta Kudu ta yi imani mutumin da aka hallaka Kim Jong-Nam ne kuma Koriya ta Arewa tana da hannu a kisan.

Shi dai Kim Jong-Nam dan shekaru 45 na zama shine babban dan marigayi Kim Jong-Il tsohon shuagban Koriya ta Arewa. An hallaka Kim Jong-Nam a filin jirgin sama na Malesiya, kuma dama tun shekara ta 2011 ya zama a Macau da ke karkashin ikon China, inda ake gani rashin kyakkyawar dangantaka da mahaifinsa marigayi shugaban kasar ya janyo aka bai wa kaninsa madafun ikon kasar ta Koriya ta Arewa.