Ana ɗaukan tsauraran matakan tsaro a birnin Kinshasa. | Labarai | DW | 20.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ɗaukan tsauraran matakan tsaro a birnin Kinshasa.

An fara ɗaukan tsauraran matakan tsaro a Kinshasa, babban birnin Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, gabannin bayyana sakamakon wucin gadi na zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ran 30 ga watan jiya. Zaɓen dai shi ne na farko a ƙasar tun shekaru 46 da suka wuce. Wasu majiyoyin hukumomin jami’an tsaron ƙasar sun ce za a tsananta matakan tsaro a birnin Kinshasan tun daga yau lahadi, tare da zuba ƙarin ’yan sanda masu sintiri a kan muhimman tituna da gine-ginen birnin. Ana dai sa ran cewa, sai an shirya zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar, inda shugaba mai ci yanzu Joseph Kabila da mataimakinsa, kuma tsohon shugaban ’yan tawaye Jean-Pierre Bemba ne za su tsaya takarar.