An zargi wasu mutane 15 a Spain da aiki irin na yan ta´adda | Labarai | DW | 19.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi wasu mutane 15 a Spain da aiki irin na yan ta´adda

Jamian yan sanda a kasar Spain naci gaba da tsare mutanen nan masu tsattsauran raayi mabiya addinin islama goma sha biyar da suka cafke da safiyar.

A wata sanarwa data fito daga ma´aikatar cikin gida ta kasar, ta nunar da cewa wadan nan mutane ana zargin su ne da bawa jamian alqeda horo tare da tura su izuwa kasar Iraqi.

Daga cikin mutanen akwai yan kasar Morocco 8 da kuma wasu daga Spain da Iraq da Masar da Faransa da Denmark da Belarus da kuma Saudi Arabia.

Kame wadan nan mutane dai na a matsayin kame n e na baya bayan nan da jamian yan sanda keyi a kasar akan masu tsattsauran raayin, a tun bayan harin bama baman nan na birnin Madrid´da yayi sanadiyyar rasuwar mutane 191.