1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Syria da rashin ba da kariya ga jakadan Turai

February 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9N
Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka sun yi Allah wadai da hare haren da aka kai kan ofisoshin jakadancin wasu kasashen Turai a kasar Syria. Shugabar majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar EU, Ursula Plassnik ta ce babu wata hujja da ta halatta kai wadannan hare haren. Ita kuwa gwamnatin Amirka ta bayyana hare haren da cewa wani abin kunya ne da Syria ta kasa ba da cikakkiyar kariya ga ofisoshin jakadancin duk da barazanar kai musu hari da aka samu tun da farko. A jiya asabar daruruwan masu zanga-zanga a Damaskus suka cunnawa ofisoshin jakadancin Denmark da na Norway wuta, don nuna fushinsu da buga zane-zanen batanci ga Annabi Mohammed SAW da wata jaridar Denmark ta fara yi, kafin wasu jaridun Turai su bi sahu.