1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi shugaba Bush da yin gaba kanshi wajen ba hukumomin leken asiri umarni

Wata jaridar Amirka ta ce shugaba GWB ya ba da umarnin sauraron hirarraki ta wayar tarho a ciki kasar ba tare da ya samu izinin kotu ba. Jaridar New York Times ta rawaito cewa bayan hare haren ranar 11 ga watan satumban shekara ta 2001, shugaba Bush ya ba jami´an leken asirin soji na hukumar tsaron kasa ta NSA umarnin sauraron hirarrakin daruruwan mutane dake buga waya ko aikewa da sakonnin E-mail daga kasar ta Amirka zuwa ketare. Kawo yanzu shugaba Bush bai musanta rahoton jaridar ba. Shugaban ya ce ba zai bayyanawa jama´a aikin da da hukumomin leken asirin ke yi ba. ´Ya´yan jam´iyun democrat da republicans sun yi kira da a gudanar da bincike akan wannan rahoto.