An zargi hukumomin Afghanistan da cin zarafin firsinoni | Labarai | DW | 13.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi hukumomin Afghanistan da cin zarafin firsinoni

Kungiyar kare hakin bil Adama ta kasa da kasa wato Amnesty International ta yi kira ga dakarun kiyaye zaman lafiya na duniya a Afghanistan wato ISAF da su daina mika firsinoni ga hukumomin kasar. A cikin wani rahoto da ta bayar kungiyar ta Amensty ta ce akwai kwakkwarar shaida da ke nuni da cewa dakarun tsaron Afghanistan na ganawa firsinoni azaba. To sai dai duk da haka rundunar ta ISAF dake karkashin inuwar kungiyar tsaro ta NATO ta ci-gaba da mikawa hukumomin leken asirin Afghanistan firsinoni. NATO ta yi watsi da wannan zargi. A wani labarin kuma Amirka ta nuna damuwa dangane da yawaitan cin hanci da rashawa da tabarbarewa tsaro a Afghanistan, tana mai cewa ba abin karbuwa ba ne. Gwamnati a Washington ta yi kira ga shugaba Hamid Karzai da ya dauki kwararan matakai.