An zargi gwamnatin Afirka Ta Kudu da rashin daukar matakar yaki da AIDS | Labarai | DW | 19.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi gwamnatin Afirka Ta Kudu da rashin daukar matakar yaki da AIDS

Wakilin MDD na musamman kan cutar AIDS a nahiyar Afirka Stephen Lewis ya yi suka da kakkausar harshe ga manufar ATK na yaki da cutar ta AIDS da kuma tsare mutane 44 dake zanga-zangar nuna adawa da wannan manufa. Mista Lewis ya ce daga cikin kasashen Afirka da ya kaiwa ziyara a cikin shekaru 5 da suka gabata, ATK ce kadai har yanzu ba ta dauki sahihan matakai don tinkarar cutar AIDS ba. Ya ce a kullum mutane 600 zuwa 800 ke mutuwa a ATK sakamakon wannan cuta mai karya garkuwar jikin dan Adam. A lokacin da yake jawabi a karshen taron MDD kan cutar AIDS a birnin Toronto na kasar Canada, wakilin na MDD ya kuma yi tir da shugabannin kasashen kungiyar G-8 saboda rashin cika alkawuran da suka dauka na taimakawa asusun yaki da AIDS.

Ya ce “Ko tantama babu, har yanzu gwamnatin ATK ba ta mayar da hankali wajen kula da ba da magunguna da masu dauke da cutar. Hakazalika ba ta daukar managartan matakai wajen yaki da yaduwar cutar a tsakanin al´umarta.”