1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Amurka da laifuka na take hakokin bil adama--

Jamilu SaniOctober 14, 2004

Kungiyar kare hakin bil adama ta HRW ta zargi Amurka da laifin cin zarafin fursinonin da ake tsare da su---

https://p.dw.com/p/BvfY
Hoto: AP

Cikin wani sabon rahoto da kungiyar kare hakin bil adama ta human Rights Watch dake mazauni a birnin New York ta fitar,ta baiyana bacewar wasu fursinoni 11 da gwamnatin Bush ta kama cikin matakan data bulo da su na yaki da aiyukan tarzoma wanda kuma hakan ke nuni da cewar tamkar gwamnatin ta Bush ta bude wasu hanyoyi ne na azabtar tare da cin zarafin fursinonin dake tsare a hanun jami’an tsaro Amurka duk kuwa da cewar tsarin dokoki na kasa da kasa ya haramta yin hakan.

Rahotan dai Kungiyar kare hakin bil adama ta Amurka ya baiyana cewar kungiyar leken asirin Amurka ta CIA sun hakikance cewar suna tsare da mutane shida da ake zargi da aiyukan tarzoma,wanda kuma aka dauki tsawon lokaci ba tare da yanke musu hukunci ba.

Bugu da kari rahotan na kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Watch ya baiyana cewar gwamnatin Amurka ta gaza yin rijistar fursinonin dake tsare da su bisa laifuka na aiyukan ta’adanci cikin jerin sunayen masu laifin da ake tsare da su,yayin kuma da ta gaza yin bayani a game da inda ake tsare da su wanda kuma hakan ke nuni da cewar an tauye musu hakokin su na samun kariya a fuskar sharia.

Kungiyar ta kare hakin bil adama ta Human Rights Watch ta nuna matukar damuwarta a game da matakai na azabtarwa da gwamnatin Amurka ke dauka kann fursinoni data ke zargin cewar yan kungiyar al-Qaeda ne,tun bayan data bulo da matakai na yaki da aiyukan tarzoma bayan harin ranar 11 ga watan Satumabar shekara ta 2001 da ya afku a Amurka.

Reed Brody lauyan dake yiwa kungiyar kare hakin bil adama ta HRH aiki,ya baiyana irin wanan matakai da gwamnatin Amurka ke dauka a matsayin wani salo na mulkin kama karya na soji,duk kuwa da cewar kasar ta Amurka na bin tafarki ne irin na Democradiya.

Sabon rahotan da kungiyar kare hakin bil adama ta HRW ta fitar ya biyo bayan rahotan da kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights First ta fitar cikin watan Yunin da ya gabata,wanda cikin rahotan nata ta nuna matukar damuwarta kann yadda Amurka ke cigaba da gina gidajen kurkuku na asiri a duka fadin kasar da jami’an tsaron asiri na Amurka suka boye mutanen da ake zargi da laifuka na yan tarzoma.

Kungiyar kare hakin bil adama ta HRW ta nuna damuwarta halin da Khalid Shiéikh Mohammad ke ciki,wanda kuma aka kama bisa zargin da ake yi masa da hanun cikin shirya makarkashiyar harin ta’dancin 9/11,wanda kuma aka baiyana cewar jami’an tsaron Amurka na gana masa matukar azaba.