AN ZABI JOSÉ MANUEL BARROSO TAMKAR SABON SHUGABAN HUKUMAR TARAYYAR TURAI | Siyasa | DW | 22.07.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AN ZABI JOSÉ MANUEL BARROSO TAMKAR SABON SHUGABAN HUKUMAR TARAYYAR TURAI

Majalisar tarayyar Turai, ta zabi tsohon Firamiyan kasar Portugal, José Manuel Barroso tamkar shugaban Hukumar kungiyar EU. Zai dai fara aiki a wannan mukamin ne a ran 1 ga watan Nuwamba. Kafin wannan lokacin kuwa, yana da gagagrumin aiki a gabansa, wato na zaban rukunin kwamishinoni 24, wadanda tare ne za su dinga tafiyar da harkokin kungiyar.

Barroso, sabon shugaban Hukumar Tarayyar Turai da Majalisar Turai ta zaba a birnin Straßburg.

Barroso, sabon shugaban Hukumar Tarayyar Turai da Majalisar Turai ta zaba a birnin Straßburg.

Da can dai, babu wanda ke goyon bayan José Manuel Barroso kamar dan takara, a zaben shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai da majalisar Turan za ta yi. Yayin da ake gabatad da `yan takara, babu sunansa a jerin sunayen da aka mika wa majalisar. Daga baya ne, bayan an kasa yarjewa kan wanda zai gaji Romano Prodi na kasar Italiya a wannan mukamin, shugabannin kasashen kungiyar, suka cim daidaito kan amincewa da shi.

Kafin zabansa a wannan mukamin da Majalisar Turai ta yi yau abirnin Starßburg dai, José Manuel Barroso, ya rike mukamin Firamiyan kasarsa ta Portugal. Shi dai Barroson, mai bin ra’ayin mazan jiya ne. Kuma ya bayyana cewa, a wannan sabon mukamin da za a nada shi, ba zai yarda kasashen Turai masu angizo a kungiyar su mai da shi karen farautarrsu ba. Bisa dukkan alamu dai, yana matashiya ne da Faransa, da Birtaniya da kuma Jamus, wadanda ke kokari a fakaice su rage ikon da shugaban Hukumar ke da shi. Tun da farko dai, Barroso ya bayyana cewa, yana son ya kasance shugaba ne mai cikakken iko, kamar yadda yarjejeniyar Kungiyar Hadin Kan Turan ta tanadar. Yana son ya yi amfani da ikonsa ne na sallamar kwamishinonin Hukumar, idan ya ga cewa, sun gaza wajen gudanad da ayyukansu.

Wannan matsayin da ya dauka dai, ya janyo masa farin jini a Majalisar Turan, musamman ma dai a gun wakilan kananan kasashen kungiyar, wadanda ke ganin cewa, manyan kasashe kamarsu Faransa da Birtaniya da Jamus, na yunkurin mamaye duk wasu harkokin kungiyar ne.

Kafin ma ya fara aiki a sabon mukaminsa a ran 1 ga watan Nuwamba mai zuwa, manazarta harkokin yau da kullum na kungiyar na hasashen cewa, wani rikici zai barke tsakanin Hukumarsa da Jamus. Dalilin haka kuwa shi ne, ya bayyana cewa, idan ya hau mukamin shugabancin Hukumar Turan, zai yi duk iyakacin kokarinsa wajen ganin cewa, an kiyaye ka’idojin kare darajar kudin nan na Euro, wadanda a halin yanzu, Jamus da wasu manyan kasashen kungiyar ke takewa.

Wannan dai na daya daga cikin abababan da za su kalubalance shi a wannan mukamin. Daya matsalar da ke nuna alamun tasowa kuma, ita ce ta yadda yake niyyar tafiyar da tsarin aikinsa, wajen jan akalar harkokin kungiyar. Jose Manuel Barroso dai ya bayyana cewa, duk kwamishinonin 25, da kasashe mambobin kungiyar za su turo zuwa cibiyar Hukumar a birnin Brussels, wato zai bukace su su nuna masa biyayya ne kamar yadda ya yi da ministocinsa a kasar Portugal. Amma haka din zai kasance wani abu ne mai wuya. Saboda, kwamishinonin, an turo su ne don su wakilci kasashensu a hukumar, su kuma kare maslaharsu, amma ba su bi umarnin wani shugaba ba.

A zaben da aka gudanar yau a Majalisar Turan a birnin Straßburg dai, Barroso ya sami kashi 60 cikin dari na kuri’un da aka ka da. Kafin ka da kuir’un kuwa, sai da aka yi muhawara a zauren Majalisar, inda wakilai suka yi wa sabon shugaban tambayoyi. A farkon jawabin da ya yi dai, Barroso, ya bayyana amincewarsa da karbar kasar Turkiyya a cikin kungiyar. Kuma ya yi kira ga inganta huldodi da kasashen yankin bahar rum.

Jose Manuel Barroso dai, ya bayyana imaninsa na cewa, shirin cim ma hadin kan nahiyar Turai gaba daya, shiri ne ingantacce kuma mai ma’ana. Sabili da haka ne yake kira ga masu tantama da wannan akidar da su sake tunaninsu, su hada gwiwa wajen cim ma wannan gurin.

To yanzu dai, kuungiyar Hadin Kan Turai ta sami sabon shugaban Hukumarta, wanda shi ne José Manuel Barroso, tsohon Firamiyan kasar Portugal. Yanzu kuwa, babu abin da ya saura kuma sai a jira a ga irin kamun ludayin da zai yi, idan ya hau mukaminsa a farkon watan Nuwamba.

 • Kwanan wata 22.07.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvhp
 • Kwanan wata 22.07.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvhp