1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi sabon shugaban Jamus

June 30, 2010

Jamus ta samu sabon shugaban ƙasa, wannan ya biyo bayan zaɓen da aka gudanar a yau

https://p.dw.com/p/O7Ju
Christian WulffHoto: AP

A yaune majalisar tarrayar Jamus ta zaɓi sabon shugaban ƙasa. Sabon shugaban shine Christian Wulff, wanda kafin zaɓen sa a wannan sabon muƙamin gwamna ne. Shugaban ƙasar wanda marar cikakken iko ne, wakilai a majalisar dokoki ta Bundestag, da kuma wakilai daga majalisun jihohine suka haɗu don zaɓar sa a yau. Haɗin gwiwar jam'iyun da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta, suna da kujeru 644 daga cikin kujeru 1244 na majalisar, don haka babu wani mamaki a nasarar da sabon shugaban Christian Wulff wanda ɗan takaransu ne ya samu. To sai dai shi ma ɗan takaran jam'iyar Social Demokrat, Joachim Gauck ya samu ƙarin karɓuwa na mamaki, abinda ya sa aka samu turjiya wajen samun wanda ya haye. Andai gudanar da zaɓen har zagaye uku, kafin a samu wanda ya yi rinjaye. Da farko Wulff ya gaza samun nasara da ƙuri'u 23, a zagaye na biyu ƙuri'u takwas suka hana shi tsallakewa. Zaɓen ya biyo bayan murabus ɗin tsohon shugaban ƙasar Horst koehler ya yi, biyo bayan sukar da aka yiwa kalamansa, na cewa kasancewar sojin Jamus a Afganistan, yana nasaba da batun tattalin arziki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal