An yiwa wasu Jamusawa biyu ´yan jarida kisan gilla a Afghanistan | Labarai | DW | 07.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yiwa wasu Jamusawa biyu ´yan jarida kisan gilla a Afghanistan

Ma´aikatar cikin gidan Afghanistan da kuma kakakin rundunar kasa da kasa ISAF sun tabbatar da cewa an kashe wasu ´yan jarida Jamusawa su biyu a wani kwantan bauna da aka yi musu a arewacin Afghanistan. ´Yan sanda suka ce ´yan jaridar namiji daya da mace daya suna aikin tattara bayanai ne a wani yanki mai tazarar kilomita 120 arewa da Kabul lokacin da aka bude musu wuta. Har yanzu dai ma´aikatar harkokin wajen Jamus ba ta tabbatar da sunayen mutanen biyu ba. Rahotanni sun nunar da cewa dukkansu biyu ´yan jarida ne masu zaman kansu dake yiwa DW aiki. A martanin farko da ta mayar gwamnatin Jamus ta yi Allah wadai da kisan ´yan jaridar. Ministan harkokin waje F.W.-Steinmeier ya ce dole ne a gudanar da cikakken bincike game da kisan jamusawan su biyu. Ya ce za´a yi farautar wadanda suka aikata wannan danya don a gurfanad da su gaban kuliya.

A wannan shekara tashe tashen hankula sun tsananta a fadi kasar ta Afghanistan musamman a kudanci da gabashin kasar inda ´yan Taliban ke fafatawa da dakarun waje da na gwamnati.