An yiwa Ariel Sharon tiyatar gaggawa a cikinsa
February 11, 2006Talla
An yiwa FM Isra´ila Ariel Sharon wani aikin tiyata na gaggawa bayan wani hoton cikinsa ya nuna wani damejin da hanjinsa dake narka abinci yayi. Kafin a yi masa aikin tiyatar na tsawon sa´o´i 4, jami´ai a asibitin sun ce rayuwar Sharon ta shiga wani mummunan hadari. Kakakin asibitin a birnin Kudus, Ron Krummer cewa yayi:
“A yau da safe halin rashin lafiyar FM ya yi muni. Saboda haka mun dauki hoton cikinsa wanda ya nuna mummunan dameji a tsarin hanjinsa shi yasa muka yanke shawarar yi masa tiyata cikin gaggawa.”
Wani na hannun damarsa ya ce an cire wani bangare na hanjinsa. Tun kimanin makonni 5 da suka Sharon mai shekaru 77 a duniya yake cikin suma na dole a asibitin Hadassah tun bayan da ya yi fama da bugun jini a ranar 4 ga watan janeru.