An yi zargin tabka maguɗi a zaɓukan ´yan majalisar dokokin Kamaru | Labarai | DW | 22.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi zargin tabka maguɗi a zaɓukan ´yan majalisar dokokin Kamaru

An kammala kada kuri´a a zabukan ´yan majalisar dokokin kasar Kameru to sai dai rahotanni sun ce mutane ba su fita sosai don kada kuri´a ba. ´Yan adawa sun yi tir da zaben wanda suka ce an tabka magudi a ciki inda aka mayar da gidajen mutane tashoshin zabe baya ga karancin takardun zabe da aka fuskanta a yankunan da ´yan adawa ke da karfi. An yi tsammanin cewa zabukan zasu karfafa mulkin shugaba Paul Biya na shekaru 25 a wannan kasa dake tsakiyar Afirka amma ´yan adawa sun yi zargin yin aringizo kuri´u yayin da masu sa ido a zabe na kasa da kasa suka kauracewa zaben sannan ´yan kasar kalilan ne suka yi rajista. Wani wakilin kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce an kada kuri´a a cikin gidan wani Basarake dake birnin Yawunde. Hakan ya saba da dokokin zabe. An yi ta fatattakar ´yan adawa a wasu yankuna na kasar.