1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi zargin aukuwar wasu abubuwa da ba su dace ba a zaben Azerbaidjan

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvMJ

Masu kare hakin jama´a a janhuriyar Azerbaidjan ta tsohuwar tarayar Sobiet sun yi zargin aukuwar wasu abubuwan da ba su dace ba a zaben ´yan majalisar dokokin kasar da ake yi yau lahadi. Amma jami´an hukumar zaben kasar a birnin Baku sun ce zaben na tafiya salin-alim ba da wata tangarda ba. A lokacin da yake kada kuri´arsa shugaba Ilkhan Aliyev mai ra´ayin rikau ya yi watsi da zargin da masu sa ido a zabe na kasa da kasa suka yi cewar an tursasawa ´yan adawa a lokacin yakin neman zabe. Kimanin mutane miliyan 5 ne suka cancanci kada kuri´a zaben majalisar dokokin mai kujeru 125. sama da jami´ai dubu daya daga ko-ina cikin duniya ke kula da yadda zaben ke gudana.