An yi zanga-zanga mafi girma a birnin Budapest na kasar Hungary | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi zanga-zanga mafi girma a birnin Budapest na kasar Hungary

Fiye da mutane dubu 15 suka shiga cikin wani gangami mafi girma a jerin zanga-zangar da aka shafe kusan mako guda ana yi a Budapest babban birnin Hungary, na neman FM Ferenc Gyurcsany da yayi murabus bayan ya amsa yin karya game da tattalin arzikin kasar. Rahotanni sun nunar da cewa an fara gangamin ne da yau da rana kuma kawo yanzu ba wani tashin hankali da ya barke. Akalla mutane 250 suka samu raunuka sannan aka kama mutane 200 sakakamon arangamar da aka shafe dere 3 a jere ana yi tsakanin masu zanga-zanga da ´yan sanda a babban birnin na Hungary. Babbar jam´iyar adawar kasar Fidesz ta soke zanga-zangar da shirya yi yau saboda fargabar barkewar wata tarzoma.