1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wata makarkashiyar kai harin ta´addanci a Jamus

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta nan Jamus ta rawaito cewar an shirya kaiwa kasar wani harin ta´addanci shigen wanda aka kaiwa birnin London a bara. Jaridar ta ce wani bincike da aka yi ya gano cewar wasu bama-bamai biyu da aka gano boye a cikin wasu jakuna a tashoshin jiragen kasa na biranen Dortmund da Koblenz cikin watan jiya, na daga cikin makarkashiyar kai harin. Jaridar mai fita kullum ta rawaito manyan jami´in tsaro da bata ambaci sunansu na bayanin haka. Jaridar ta kuma jiyo daya daga cikin jami´an na cewa karfin bama-baman ka iya janyo mummunar asara kamar yadda aka fuskanta a hare haren ta´addancin da aka kaiwa birnin London a cikin watan yulin bara.