1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wata girgizar ƙasa cikin teku a Indonesiya.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupZ

A ƙasar Indonesiya, inda igiyar ruwan nan ta tsunami ta janyo asarar rayukan ɗimbin yawan mutane a kan tsibirin Java, an sake yin wata girgizar ƙasa a ƙarƙashin teku, a tsibirin Sulawesi, abin da ya janyo fargabar aukuwar wata annobar kuma ta tsunami. Wani jami’in kula da yanayin sararin samaniya na ƙasar ya faɗa wa maneman labarai cewa, an gano cibiyar girgizar, wadda ta kai ƙarfin awo 6 da ɗigo 6 a mizanin Richter, a wani wuri ne mai nisan kilomita 90 a kudu maso gabashin birnin Gorontalo.