An yi wani gumurzu a teku tsakanin sojoji da ´yan tawaye a Sri Lanka | Labarai | DW | 02.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wani gumurzu a teku tsakanin sojoji da ´yan tawaye a Sri Lanka

Dakarun ruwa na gwamnatin Sri Lanka da ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers sun gwabza wani kazamin fada a cikin teku har izuwa asubahin yau. Rundunar sojin kasar ta yi ikirarin nitsad da kwale kwale 8 na ´yan tawaye sannan ta kashe ´yan tawaye guda 80. wani jami´i a ma´aikatar tsaron kasa ya ce fadan ya barke jiya daddare lokacin da wasu kwale kwale kusan 20 mallakin ´yan tawayen na Tamil suka kai hari kan wasu sojojin ruwa dake sintiri a kusa da tashar jirgin ruwa ta Kanka-Santhurai dake can gabashin tsibirin Jaffna. Jami´in ya ce ´yan tawaye sun lalata jiragen ruwan yaki guda biyu yayin da sojoji biyu kuma suka jikata. To amma ´yan tawayen sun ikirarin nisad da jiragen ruwan sannan kimanin sojojin ruwa 30 sun bace.