An yi wani batakashi tsakanin sojin Isra´ila da Hisbollah a gabashin Libanon | Labarai | DW | 19.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wani batakashi tsakanin sojin Isra´ila da Hisbollah a gabashin Libanon

Sojojin Isra´ila sun kaddamar da wani samame ta sama a kan wani sansanin mayakan Hisbollah dake gabashin Lebanon. Rundunar sojin Isra´ila ta tabbatar da kai wannan farmaki, inda ta kara da cewa an halaka sojinta daya sannan biyu sun samu raunuka a fafatawar da suka yi da ´yan yakin sunkurun Hisbollah. Rundunar ta ce an kai samamen ne a kusa da garin Baalbek da zummar katse hanzarin jigilar makaman yaki ta ruwa daga Syria da Iran zuwa ga ´yan Hisbollah. Wannan dauki ba dadin dai shi ne na farko tsakanin sassan biyu tun bayan da wani shirin tsagaita bude wuta ya fara aiki a ranar litinin da ta gabata. A cikin wata sanarwa da ya bayar FM Libanon Fuad Siniora ya zargi Isra´ila da karya shirin tsagaita wutar inda ya ce zai mika wannan batu gaban babban sakataren MDD Kofi Annan.