1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wani artabu tsakanin sojojin gwamnati da ´yan Tamil a Sri Lanka

Ƙungiyar Saudiyya

Ƙungiyar Saudiyya

Akalla mutane 40 daukaci ´yan tawaye rahotanni suka ce sun mutu bayan da mayakan kungiyar Tamil Tigers suka kaddamar da wani hari ta ruwa akan dakarun gwamnatin Sri Lanka. Rundunar kasar ta ce an kashe sojin ruwa 4 sakamakon wannan hari. A gumurzun wanda aka yi a yankin gabar teku mai nisan kilomita 320 arewa da babban birnin kasar Colombo, an nutsa da kananan jiragen ruwa 4 na ´yan tawaye. Dakarun gwamnati dai sun yi ta kai farmaki ta sama tun bayan da wata nakiyar karkashin kasa ta halaka mutane 64 da ke tafiya a cikin wata safa a ranar alhamis da ta gabata. Tun a farkon watan afrilu mutane kimanin 700 suka rasu bayan da rikici ya kazance a kasar ta Sri Lanka musamman a arewacin kasar, inda ´yan Tamil Tigers ke neman ballewa don kafa kasarsu.