An yi wa Yahoo sabon kutse | Labarai | DW | 15.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa Yahoo sabon kutse

Kamfanin Yahoo ya sanar da bankado wani sabon kutse da masu satar bayanai suka yi masa kan manahajojinsa a shekara ta 2013.

Kamfanin sadarwa na Yahoo ya sanar da bankado wani sabon kutse da masu satar bayanai suka yi a cikin manahajojinsa. Kamfanin ya bayyana cewa lamarin wanda ya wakana a shekara ta 2013 ya shafi bayanan mutane sama da miliyan dubu masu amfanin da hanyar sadarwar ta Yahoo, wanda ke kasancewa satar bayanan fasaha mafi girma da kamfanin ya taba fuskanta a tsawon tarihinsa. 

Kamfanin wanda ke shirin sayar da sashen ayyukansa na fannin sadarwa na intanet ga kamfanin Verizon Communication a kan tsabar kudi kusan biliyan biyar na dalar Amirka, ya bayyana cewa wannan sabon kutse da ya bankado ya sha bambam da wanda ya wakana a watanni uku da suka gabata wanda ya shafi mutane akalla miliyan 500 masu mu'amala da shafin na Yahoo. Ya zuwa yanzu dai kamfanin na Yahoo ya ce bai kai ga gano wadanda suka yi masa wannan kutse ba.